An daura auren zawarawa dari a Kano

Angwaye
Image caption Wadansu daga cikin angwayen

A yau Talata ne aka daura auren zawarawa dari tare da angwayensu a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Hukumar Hisbah ta Jihar ce dai ta dauki alhakin gudanar da bikin a madadin gwamnatin jihar, a karo na farko a tarihin jihar.

Auren na cikin shirin aurar da zawarawa guda dubu da gwamnatin ta dauki aniyar yi.

Tuni dai an yi wa zawarawan da mazajen da za su aura lacca a kan muhimmancin zaman aure; sannan an gudanar da gwajin cutar kanjamau don tabbatar da lafiyarsu.

Hukumar ta Hisbah ta ce ta bullo da shirin ne don rage mutuwar aure da sanya tarbiyyya a tsakanin al'ummar Jihar.

Karin bayani