Za a rataye matashin da ya kashe iyayensa

Bello Garba (Baba)
Image caption Matashin da aka yankewa hukuncin rataya, Bello Garba

Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Nigeria ta yankewa wani matashi mai suna Bello Garba wanda aka fi sani da Baba hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samunsa da laifin kashe iyayensa, da yan uwansa uku.

Kotun ta ce shedun da aka gabatr mata sun tabbatar da cewa matsahin mai kimanin shekaru Ashirin da Biyar ne ya kaseh mutanen gidan nasu da suka hadar da iyayensa da wani kaninsa namiji, da kuma wasu kannensa biyu mata ciki har da mais shekaru Biyar a ranar 13 ga watan Satumbar 2010.

Mutane shida ne dai suka ba da sheda gaban kotun wadanda suka hadar da wani yaro mai shekaru 11 wanda kanine ga wanda ya aikata laifin, da kuma kanwa ga mahaifiyar wanda ya yi kisan.

Bayan kotun ta ce ta samu matashin da laifi, lauyansa ya yi rokon ta yi masa sassauci ganin cewa shi kadai ne ya rage cikin mutanen gidansu, in aka debe kaninsa; amma kotun ta ce sai dai a mika wannan bukata inda ya dace.

Kotun dai ta yankewa matshin hukuncin kisa ta hanyar rataya ne a kan kowanne kisa da aka aikata.