A taro kan matsalar tsaro na yankin Sahel

mahammadou issoufou
Image caption Shugaban Nijer, Mahammadou Issoufou

A jamhuriyar nijar an soma fara taron kasa da kasa kan matsalar tsaro a kasashen yankin Sahel.

Taron, wanda ya hada kwararrun jami'ai na da burin samar da matakai na hadin gwiwa musamman game da abin da ya shafi tsaron iyakoki, domin shawo kan matsalar ta'addanci a cikin kasashen yankin sahel.

Wata kungiya mai suna Sahel Capacity 'Building Working Group' ce ta shirya taron da hadin gwiwar gwamnatocin kasashen Amurka da Nijar.

A watan nuwamban bara ma kungiyar ta shirya irin wannan taron a kasar Algeria.

Karin bayani