Hollande ya gana da Angela Merkel a Jamus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Angela da Hollande

Sabon shugaban kasar Faransa François Hollande, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun sha alwashin yin aiki tare don kawo karshen matsalar kudi ta tarayyar turai.

A wani taron manema labarai da suka yi a Berlin, sun amince da yin aiki tare akan shawarwarin da za a gabatar a taron EU.

Sai dai Mr Hollande ya sake jaddada cewa ya na bukatar a sake nazari kan yarjejeniyar kudi da tarayyar turai ta kulla kan kasafin kudi, wanda Mrs Merkel ta goyi baya, don samar da wata manufa ta ci gaba.

Mr Hollande dai zai isa kasar Amurka ranar Jumaa don halartar taron Kasashe masu karfin tattalin arziki na G8 a Washington.

Karin bayani