Charles Taylor zai yi jawabi a kotu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption charles Taylor

Tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor, zai yi jawabi a yau, a kotun kasa da kasa dake Hague wadda ta same shi da laifin aikata laifukan yaki a kasar Saliyo.

Wannan ce damar sa ta karshe da zai yi magana a kotun ta musamman kafin yanke masa hukunci a karshen wannan wata.

Wakilin BBC ya ce a shekarun da ya shafe a matsayin dan tawaye, sannan a matsayin shugaban kasar Liberia, Charles ya iya magana kuma ya iya fitowa. Don haka watakila ya yi amfani da wannan basirar a matsayin dama ta karshe ya yi jawabi ga duniya.

Masu gabatar da kara za su nemi ya shafe shekaru tamanin a gidan kaso, yayinda lauyoyin dake kare shi kuwa suka ce wannan ma abin dariya ne.

Karin bayani