Charles Taylor ya fara kare kansa a kotu

Charles Taylor Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor

Tsohon shugaban kasar Liberia wanda kotu ta samu da aikata laifuffukan yaki, Charles Taylor, ya fara jawabin kare kansa.

A wata magiya ga kotun duniya dake Hague, Mista Taylor ya ce an biya mutanen da suka bayar da shaida a kansa, ko an tursasa su, ko kuma an yi barazanar hukunta su idan suka ki bayar da shaidar.

A cewarsa, ya yi Allah-wadai da duk wani rashin imani da aka aikata a fadin duniya.

Alkalai a Kotun Musamman mai Hukunta Laifuffukan da aka Aikata a Saliyo sun yanke hukuncin cewa tsohon shugaban na Liberia ya taimakawa 'yan tawaye masu dauke da makamai yayin yakin Saliyo, su kuma sun saka masa da daimon din da aka hako ta hanyar bautatar da mutane.

Masu shigar da kara dai sun bukaci a yanke masa hukuncin zaman kaso na shekaru tamanin.

Karin bayani