An kusa kama madugun 'yan tawayen Congo - Ocampo

Hakkin mallakar hoto
Image caption masu gudun hijira a Congo

Babban mai shigar da kara na kotun kasa da kasa wato ICC, Luis Moreno Ocampo ya ce nan ba da jimawa ba za'a kama madugun 'yan tawayen Jamhuriyyar Democradiyyar Congo, Bosco Ntaganda.

Bosco Ntaganda dai kotun na nemansa ruwa a jallo saboda zargin da ake masa na cin zarafin dan Adam.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta fitar da rahoto da yake cewa dakarun masu tada kayar baya na tilasta wa kananan yara har yan shekaru goma sha biyu shiga cikinsu su yi yaki.

Mai gabatar da kara na ICC ya ce tun shekara ta dubu biyu da shida aka bada sammacin kama madugun 'yan tawayen.

Tun farko dai Majalisar Dinkin Duniya da take kula da 'yan gudun hijira ta ce fada tsakanin sojin gwamnati da na 'yan tawaye ya tilasta wa dubban mutane tserewa zuwa makwabtansu galibinsu mata da kananan yara.

Karin bayani