Za a rage albashin ministoci da na shugaban kasa a Faransa

Francois Hollande Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Francois Hollande

Rage kashi talatin cikin dari na albashin Ministocin kasar Faransan dai daya ne daga cikin matakan da sabon shugaban kasar Francois Hollande ya ce zai dauka da zarar ya kama aiki.

Daga cikin matakan da aka amince da su a taron farko na Majalisar zartarwar kasar sun hada da rage yawan ma'aikatan dake aiki tare da ministoci da kuma wani kundin ka'idojin aiki da kowane daga cikin ministocin talatin da hudu suka sanya hannu a kai.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Hollande ya rage kudaden albashin ne domin ya nuna bambamcin dake tsakaninsa da tsohon shugaban kasar Nicolas sarkozy, wanda a lokacinsa, aka kara yawan albashin sa da kimanin kashi dari da saba'in inda ya rika karbar kusan dala dubu dari uku a kowace shekara tun bayan da ya dare kan karagar mulki a shekarar 2007.

Karin bayani