Girka: Tsipras ya zargi Merkel kan wasa da rayukan al'umma

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tsipras

Shugaban masu ra'ayin kawo sauyi a Kasar Girka Alexis Tsipras ya zargi kungiyar tarayyar turai da shugabar Jamus Angela Merkel da wasa da rayukan alummar tarayyar turai saboda dagewa da suka yi kan matakin tsuke bakin aljihun gwamnati.

An yi hasashen cewa Jam'iyyar Mr Tsipras ce za ta zo ta daya a sabon zaben da za a yi ranar sha bakwai ga watan Yuni, inda suke son sake duba batun ceto kasar Girka da kasashen waje suka yi.

Shugaban Mr Tsipras yana son kawo karshen zaftare kashe kudaden gwamnati wanda aka kakabawa kasar ta Girka don samun tallafi na kudade mai tarin yawa.

Tsipras ya shaidawa BBC cewa matakin tsuke bakin aljihun zai rusa kudin tarayyar turai na bai daya.

Karin bayani