An dage shari'ar Ratko Mladic a Hague

Ratko Mladic
Image caption Tsohon jagoran Serbiyawan Bosnia, Ratko Mladic, a kotu

An dage shari'ar tsohon jagoran Serbiyawan Bosnia, Ratko Mladic, wanda aka tuhuma da aikata laifuffukan yaki.

Alkalin da ke shugabantar zaman kotun a Hague ya ce an yi hakan ne don a baiwa alkalan damar bincika kurakuran da masu shigar da kara suka yi yayin bayyana shaidunsu ga lauyoyin da ke kare wanda ake tuhuma.

Ba a tabbatar da ranar da za a ci gaba da sauraron karar ba.

Janar Mladic na fuskantar zarge-zargen aikata laifuffukan yaki da laifukan cin zarafin bil-Adama wadanda suka danganci yakin Bosnia, to amma ya musanta zarge-zargen.

Karin bayani