Shari'ar Mladic za ta maida hankali kan kisan kiyashi

Image caption Mladic

Masu gabatar da kara a shariar tsohon kwamandan dakarun sabiyawan Bosnia Ratko Mladic a Hague, za su maida hankali ne a yau kan kisan kare dangin da aka yi a Srebrenica cikin shekarar 1995.

Musulmi maza da yara kanana fiye da dubu bakwai ne aka halaka a kisan gilla mafi muni da aka taba yi a nahiyar turai tun bayan yakin duniya na biyu.

Janar Mladic na fuskantar zarge zargen aikata laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adama, to amma ya musanta zarge zargen.

Saboda a fara shari'ar ta sa da wuri sai da aka zaftare tuhume-tuhmen da ake masa da kusan rabi.

Karin bayani