Gwamnonin Arewa na taron duba matsalolin yankin

Jami'an kwana-kwana a wani waje da bom ya tashi a Kaduna kwanakin baya
Image caption Jami'an kwana-kwana a wani waje da bom ya tashi a Kaduna kwanakin baya

A yau ne ake sa ran gwamnonin Arewacin Nigeria za su gudanar da wani taro a Kaduna dake arewacin kasar don yin nazari game da irin matsalolin da yankin ke fuskanta.

Daya daga cikin manyan kalubale ga yankin shi ne na tabarbarewar tsaro.

Gwamnonin na sa ran duba hanyoyin magance matsaloli da suka hada da na tsaron da ma wasu batutuwan da suke ciwa yankin tuwo a kwarya.

Daga cikin wasu jerin matsalolin dake addabar yankin akwai batun harkar noma.

Karin bayani