Gwamnonin Arewa sun kammala taronsu a Kaduna

Harin da aka kai a Kaduna a kwanan baya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harin da aka kai a Kaduna a kwanan baya

Gwamnonin arewacin Najeriya sun bayyana cewar a shirye suke su dauki matakan bai daya don tunkarar matsalolin tsaro a yankin.

Gwamnonin wadanda a yau suka yi wani taro a Kaduna sun ce wasu matsalolin tsaron da suka tattauna a kai sun hada da yawan tashe tashen hankula a yankin da kuma batun rikicin manoma da makiyaya.

Hakazalika, gwamnonin sun sha alwashin daukan matakai na farfado da harkar noma da kiwo a Arewacin Najeriya, wanda kafin a gaano man fetur a kasar, shi ne ginshin tattalin arzikin Najeriya baki daya.

Sai dai kuma 'yan Arewacin Najeriya da dama suna ganin cewa an dade ana ruwa kasa na shanyewa domin kuwa gwamnonin sun sha gudanar da irin wannan taro a baya, amma har yanzu mazauna yankin na fama da kangin tallauci da kuma rashin tsaro .

Karin bayani