Save the Children ta yi gargadi kan yunwa a Nijer

Image caption Shugaban Nijer Issoufou

Kungiyar agaji ta Save the Children, ta yi gargadin cewa matsalar abinci a jamhuriyar Niger dake yankin yammacin Afirka na neman shiga matsanancin hali.

Kungiyar ta ce adadin yara dake bukatar kulawar lafiya sakamakon karancin abinci na rasuwa saboda yunwa.

An gargadi kungiyoyin bada agaji game da Niger tun watanni da dama da suka gabata, sakamakon karancin ruwa wanda ya haddasa karancin cimaka da tsadarsa.

Mutane fiye da miliyan shida ne alamarin ya shafa a Niger, kuma kungiyar agajin ta ce matsalar na ci gaba da yaduwa zuwa wasu kasashen yankin Sahel.

Karin bayani