Wani abu ya tarwatse da 'yan fashi a Fatakwal

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

'Yansanda sun ce akalla mutane biyu wadanda ake zargin 'yan fashi ne sun rasa rayukansu bayan wani abu da suke dauke da shi ya fashe a birnin Fatakwal da ke yankin Neja Delta a Najeriya.

Wakilin BBC a wurin da al'amarin ya faru ya ce motar safar da mutanen ke tafiya a ciki ta yi kaca-kaca.

Wadansu mutanen biyu kuma suna asibiti a kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Ya jaddada cewa babu dalilin da zai sa a yi zargin fahewar abin na da alaka da kungiyar Boko Haram.

A 'yan shekarun nan dai kungiyar ta Boko Haram ta kaddamar da hare-hare da dama a arewacin Najeriya, amma ba ta kai hari a kan masana'antun man kasar da ke kudanci ba.

Wadansu kungiyoyin mayakan sa kai kan kaddamar da hare-hare ba kakkautawa a kan masana'antun man da ke Fatakwal da ma sauran yankunan da ke kewaye da birnin, amma da damansu sun shiga shirin gwamnati na yin afuwa don haka hankali ya dan kwanta a yankin.

Wakilin BBC, Abdul Mohammed Isa, ya ce al'amarin ya faru ne kusa da tsakiyar birnin, inda mutane suka yi cincirindo suna kallo.

Karin bayani