Amurka na kokarin saka 'Boko Haram' cikin 'yan ta'adda

boko haram Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Imam Abubakar Shekau

Rahotanni daga Amurka na cewa ma'aikatar shari'ar kasar na kara sa matsin lamba kan ma'aikatar harkokin wajen kasar da ta sanya kungiyar nan ta Jama'atu Ahlil Sunnah Lidda'awati Wal Jihad da ake kira Boko Haram a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda na kasashen waje, saboda hare-haren kashe jama'a da ake zargin kungiyar da kai wa a Najeriya.

To sai dai kuma wasu mjiyoyi daga Amurkar na cewa ma'aikatar harkokin wajen na yin biris da wannan bukata, inda bayanai ke cewa ta na kamun kafa a majalisar dokokin Amurkar domin kada a kafa wata dokar da zata bada damar sanya kungiyar a cikin jerin kungioyoyin yan ta'adda.

Bisa dukkan alamu dai batun na sanya kungiyar ta Jama'atu Ahlil Sunnah Lidda'awati wal jihad da mutane ke wa lakabi da Boko Haram a cikin jerin kungiyoyin ta'addanci na kasashen waje, ya haifar da bambance-bambancen ra'ayi a cikin gwamnatin Amurkar.

Ita dai ma'aikatar harkokin shari'a ta kasar Amurka, a cewar rahotanni ta tsaya ne kai da fata domin ganin sanya kungiyar dake Najeriya a cikin jerin kungiyoiyn ta'adda na kasa da kasa, inda wata takarda da kamafanin dillancin Labaru na Reuters ya samu, ta ce yanzu haka ma'aikatar harkokin wajen kasar na fuskantar matsan lamba daga ma'aikatar da shari'a kan lallai ta sanya Boko Haram cikin kungiyoyin ta'adddaci.

A cewar rahotanni, har ma shugabar sashen tsaron kasa na ma'aikatar tsaron Amurkar, Lisa Monaco, ta rubuta watya wasika zuwa ga shugaban yaki da ta'addanci na ma'aikatar harkokin wajen kasar, Daniel Bnejamin, game da bukatar tare da matsin lamba.

To sai dai kuma bayanai sun ce ma'aikatar harkokin wajen Amurkar a nata bangare, tana can tana kamun kafa a majalisar wakilan Amurkar, domin kada a kafa wata doka ta zata bada damar sanya kungiyar ta jama'atu Ahlil Sunnah Liddd'awati Wal ihad a cikin kungiyoyin ta'addan na kasa da kasa.

A cewar kamfanin dillancin labaru na Reuters, Wani babban jami'I na ma'aikatar harkokin wajen Amurkar, ya fadi cewa ma'aikatar harkokin wajen ba jan kafa take yi kan batun ba, a a, abinda take la'akari da shi ne, sanya kungiya cikin jerin kungioyin yan ta'adda wani tsari ne mai wuyan azanci, don haka suna kokari ne a yi abinda za a iya tsayawa a gaban shari'a a iya karewa.

Bisa al'ada dai, idan Amurka ta sanya kungiya a cikin jerin kungiyin ta'addaci, to tana da iko da rika sa ido a kan aikace-kaikcen kungiyar, da yayanta, da masu taimaka mata, da kuma kamawa da tsare duk wanda ake zargi da hannu a lamauran kungiyar.

To sai dai kuma wani batu daya dade yana haifar da cece-kuce a duniya shi ne ma'anar ta'addanci, inda kungiyoyin da hukumomi ke masu kallon yan ta'adda su suna daukar kansu a matsayin masu fafutikar kwato yanci daga masu zaluntarsu, kuma hatta masana da marubuta kawo yanzu sun kasa cimma yarjejeniya kan ainihin ma'anar kamar ta ta'addaci.

Karin bayani