Dakarun ECOWAS sun isa Guinea Bissau

guinea Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jamian kasar Guinea Bissau a taron ECOWAS

Kashin farko na dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS zuwa Guinea Bissau sun sauka a kasar.

Babban aikin da za su gudanar, baya ga sa ido ga daidaituwar al'amurra, shi ne farfado da mulkin farar hula.

Dakaru 70 ne daga Burkina Faso suka fara sauka, a yayinda sauran kasashe kamar Najeriya suka ce sun kammala dukkan shirye-shiryen tura sojojin na su kuma a yanzu haka suna jiran umurni ne daga Kungiyar ta ECOWAS.

Adadin dakarun kiyaye zaman lafiyar dari shidda ne aka shirya kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrikar ECOWAS za ta tuura zuwa kasar ta Guinea Bissau.

Karin bayani