'Watakila arewa ta dunkule a shekara ta 2015'

Muazu Babangida Aliyu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnan jihar Nije, Muazu Babangida Aliyu

A Najeriya, ana cigaba da zazzafar mahawara akan batun shugabancin kasar, duk da cewar akwai sauran lokaci kafin zaben shugaban kasar a shekara ta 2015.

A ranar Alhamis gwamnonin jihohin arewacin kasar suka yi wani taro a Kaduna, inda aka ambato shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Niger, Dr Muazu Babangida Aliyu na cewar watalika arewacin Najeriyar ta fitar da dan takarar guda daya a zaben na 2015.

Rahotanni sun kuma ambato Dr Muazu Babangida Aliyu na cewar bukatar al'ummar yankin shi ne abinda suka sa a gaba, kuma zasu yi kokarin ganin sun cimma bukatarsu.

Batun mulki a Najeriya, lamari ne dake cigaba da janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan kasar, a yayinda kowane bangare a yanki ke ganin cewar shine ya kamata ya shugabanci kasar a shekara ta 2015.

Shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan wanda ke wa'adin mulkinsa na farko, bai bayyana ko zai tsaya takara a 2015 ko kuma ba zai tsaya ba.

Karin bayani