Kamfanin Spain ya soke kwantaragin gas

Image caption Sarauniyar Spain

Babban kamfanin mai na kasar Spaniya Repsol, ya amince da soke wani kwantaragin samar da iskar gas ga kasar Argentina a watannin da ake matukar sanyi.

Kamfanin na gab da samar da iskar gas din kimanin jiragen ruwa tamanin ga Argentina tsakanin watannin Yuni da Satumba.

Kamfanin na Repsol ya dauki wannan matakin ne saboda zargin kamfanin cikin gidan Argentina na Enarsa da keta kaidojin kwantaragin.

Kasar Argentina dai ta dogara ne da kashi talatin cikin dari na iskar gas din ta daga ketare.

Sanarwar na zuwa ne wata guda bayanda gwamnatin shugaba Cristina Fernandez, ta bada sanarwar kwace kadarorin kamfanin na Repsol a Argentina.

Karin bayani