Zanga zanga kan matsin tattalin arzuki

Wani mai zanga zanga a Frankfurt Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai zanga zanga a Frankfurt

'Yan sandan Jamus sun ce mutane dubu ashirin da ke kyamar shirin matsin tattalin arziki na kasashen Euro, sun yi zanga-zanga a babban birnin kasuwancinn kasar na Frankfurt.

Masu zanga-zangar suna rike da kwalayen da aka rubutua, "Kasashen Euro sun ruguje".

An tsare daruruwan masu zanga-zanga a jiya a birnin na Frankfurt a wata zanga-zangar da ba a ba da iznin yin ta ba, a kusa da hedikwatar Babban Bankin Turai.

Karin bayani