Allah Ya yi wa Al Magrahi rasuwa

Al Magrahi
Image caption Al Magrahi

Dan Libiyar nan da kotu a Scotland ta samu da laifin dana bom a jirgin saman da ya fashe a sararin samaniyar Lockerbie a 1988 ya rasu.

Abdulbasit Ali Al Magrahi shi ne kadai mutumin da kotun ta samu da lafin dana bom din, wanda ya kashe mutane dari biyu da saba'in.

An yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai ne a shekara ta 2001, amma sai aka sake shi shekaru ukku baya bisa dalilan jin kai. An ce yana fama ne da cutar sankara da ke kan hanyar kaiwa ga ajalinsa.

Sai dai sakin nasa ya samu rashin amincewa, musamman daga Amurka, inda har Shugaba Obama ya kira sakin a matsayin kuskure.

Harin bom din da ya yi sanadiyar fashewar jirgin saman kamfanin PanAm na Amurka ne a garin na Lockerbie.

Karin bayani