Taron G8 kan Afghanistan

Sakatare janar na NATO  a Afghanistan
Image caption Sakatare janar na NATO a Afghanistan

Shugaba Obama na Amurka ya yi gargadin cewa lokaci mai wuyar sha'ani yana tafe a Afghanistan.

Ya fadi haka ne a birnin Chicago na Amurka, a wajen taron kolin kungiyar tsaro ta NATO don hikimar da za a yi aiki da ita a gaba a kan Afghanistan.

Inda ya ce ya yi amannar kungiyar ta NATO tana kan hanyar da ta dace.

Ya ce, "Dukkanmu mun fahimci cewa har yanzu da sauran aiki a gaba, akwai kuma manya-manyan kalubale a gaba. Ana ci gaba da zubar da jini a Afghanistan."

A nasa jawabin, Shugaba Karzai ya ce Afghanistan ta zo taron kolin ne a matsayin kasa mai 'yancin kanta, ba wadda take a matsayin nauyi a kan kasashen duniya ba.

Karin bayani