Lokaci mai wuyar sha'ani na tafe a Afghanistan - Obama

Mahalarta taron NATO Hakkin mallakar hoto BBC Pashto
Image caption Mahalarta taron NATO

Shugabannin kungiyar tsaro ta NATO na taro a birnin Chicago na Amurka domin samar da matsaya kan yadda dangantakarsu za ta kasance da kasar Afghanistan bayan shekarar 2014, da kuma tattauna yadda NATO za ta janye daga kasar ta Afghanistan.

Sai dai har yanzu babu wata yarjejeniya da aka cimma da shugban Pakistan a kan sake bude hanyoyin isar da kayayyakin da sojojin NATO ke bukata zuwa Afghanistan ta iyakokin Pakistan din.

A Yau pira ministan Burtaniya David Cameron zai gana da shugaban Afghanistan Hamid Karzai, a yayinda kungiyar ta NATO ke mayar da hankali a kan hanyoyin da za ta bi wajen janye dakarunta daga Afghanistan, ta hanyar tabbatar da cewa akwai tsari a kasa da zai tabbatar da dorewar tsaro a kasar bayan dakarun NATON sun janye.

Kasashen da ke kawancen na fatan cimma wata matsaya a kan adadin kudaden da kowaccensu za ta rika samarwa don biyan bukatun dakarun na NATO bayan shekarar 2014.

Wuyar Sha'ani

Shugaba Obama na Amurka ya yi gargadin cewa lokaci mai wuyar sha'ani yana tafe a Afghanistan.

Shugaba Obama ya ce ya yi amannar cewa kungiyar ta NATO tana kan hanyar da ta dace.

"Dukkanmu mun fahimci cewa har yanzu da sauran aiki a gaba, akwai kuma manya-manyan kalubale a gaba. Ana ci gaba da zubar da jini a Afghanistan," in ji Mista Obama.

A nasa jawabin, Shugaba Karzai ya ce Afghanistan ta zo taron kolin ne a matsayin kasa mai 'yancin kanta, ba wadda take a matsayin nauyi a kan kasashen duniya ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Pakistan Zardari da Sakatariya Clinton

Sai dai wani batu da ke kokarin kawo tarnaki ga ci gaban da za a iya cimmawa a wajen taron shi ne, takun sakar dake tsakanin kungiyar ta NATO da kasar Pakistan wadda shugabanta Zardari ya amsa goron gayyata a kurarren lokaci domin halartar taron na Chicago.

Ana ganin kasar sa amatsayin wani bangare na matsalolin da Afghanistan ke fuskanta, sai dai har yanzu ana samun tafiyar hawainiya wajen sake bude hanyoyin samarwa dakarun NATO kayayyakin ta kan iyakokin Pakistan.

Shugaba Zardari zai gana da Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton a ranar Litinin, sai dai babu wanda yake tsammanin ganawar tasu ta warware tankiyar da ake fama da ita a kan batun, yayinda Pakinstan ta kara yawan kudaden da za a biya a kan kowacce motar kayan, sannan da tattaunawa a kan kawo karshen hare-haren jiragen da basu da matuka da Amurka ke kaiwa a cikin kasar ta.

Karin bayani