Masu zanga-zanga sun afka ma fadar shugaban kasa a Mali

Fadar shugaban kasar Mali Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fadar shugaban kasar Mali

Daruruwan masu zanga-zanga a Mali sun kaiwa shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar, Dioncounda Traore hari inda suka lakada masa dukan tsiya.

Gungun masu zanga-zangar dai sun aukawa fadar shugaban kasar dake birnin Bamako ne domin nuna fusatarsu da wani shirin kungiyar ECOWAS da ya tsawaita wa'adin mulkin Mr Traore din daga kwanaki arba'in zuwa shekara guda.

Rahotanni na nuna cewa, an jikkata shugaban rikon kwarya na Malin ne a ka, kuma wata majiyar bangaren kiwon lafiya na cewa, an garzaya da shi asibiti ne a galabaice.

Sai dai wasu rahotanni da dumi-dunmisu sun ce yanzu haka an sallami Mr Traore din daga asibiti, bayan da gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ranikan da ya samu ba munanan ba ne.

Likitan da ya duba shi ya ce an tafi da shi cikin wata mota zuwa wani wuri mai cikakken tsaro.

Wadanda suka shaida al'ammarin da idanusnu, sun ce sun ji karar harbin bindigogi, kuma wani kakakin soja ya yi ikirarin cewa masu tsaron lafiya shugaban kasar sun hallaka mutane 3.

Karin bayani