Akwai sauran aiki ta fannin ilimi a Nijar

Shugaban kasar Nijar
Image caption Shugaban kasar Nijar

A jamhuriyar Nijar, yau ne kawancen kungiyoyin farar hula masu aiki a fannin ilmi, da ake kira OPEN tare da hadin guiwar gwamnatin Nijar da ma abokan arziki masu hannu da shuni suka shirya wani babban taro kan ilimi a kasar ta Nijar.

Makasudin taron dai shi ne yin nazari a kan halin da ake ciki a nijar din game da shirye shiryen da kasar ke yi na zuwa taron duniya game da muradan karni na shekara ta 2015.

Duk da cewa gwamnatin Nijar na cewa ta yi kokari wajen kyautata yanayin ilmi a kasar, amma wasu na ganin da sauran aiki a gabanta, musamman ta bangaren koyarda harsunan kasar a makarantu tun daga tushe.

Karin bayani