Zargin yunkurin kai hari a Abuja

'Yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rohotannai daga Najeriya na cewa 'yan sanda sun kama wani mutun dazu a Abuja babban birnin kasar, dauke da makamai da wasu abubuwa masu fashewa.

An kama mutumin ne a lokacin da ya je shiga cikin harabar Radio House, wajen da ake wani taro na tsawon wata guda, inda ministoci ke bayyana irin ayyukan da suke a ma'aitatunsu.

Kuma a lokacin da lamarin ya faru akwai ministoci uku da suka hada da na yada labarai, Labaran Maku, da ta sufirin jiragen sama, Stella Oduah-Ogiemwonyi, da ministan harkokin matasa da wasanni, Bolaji Abdullahi.

Rahotanni sun ce an kama mutumin mai suna John Akpabu, da wasu abubuwan fashewa a cikin jaka.

Tuni dai jami'an tsaron da su ka kama shi sukai awon gaba da shi, inda za'ai masa tambayoyi.

Karin bayani