An yankewa wasu 'yan sandan hukuncin dauri a Masar

Masu zanga-zanga a Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Masar

Wata kotu a Masar ta yankewa wasu 'yan sanda biyar hukuncin zaman gidan kaso saboda rawar da suka taka wajen kashe masu zanga-zanga a lokacin yunkurin kawar da gwamnatin Hosni Mubarak a shekara ta 2011.

An dai yankewa 'yan sandan hukuncin zaman gidan kaso na shekaru goma.

An kuma yankewa wasu 'yan sandan biyu hukuncin jeka ka gyara halinka, yayin da aka saki wasu 'yan sandan goma.

Wannan dai shi ne hukunci na farko da aka yankewa 'yan sanda da aka zarga da alhakin kisan daruruwan masu zanga-zanga a bara a kasar ta Masar.

Karin bayani