An sallamo shugaban Mali daga asibiti bayan ya sha duka

Fadar shugaban kasar Mali Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fadar shugaban kasar Mali

Pira Ministan kasar Mali ya yi kiran da a kawo karshen zanga-zangar da ake yi a kasar bayan masu bore sun aukawa fadar shugaban kasar inda suka lakada masa duka.

Daruruwan masu zanga-zanga ne dai suka kaiwa shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar, Dioncounda Traore hari inda suka lakada masa dukan tsiya.

Gungun masu zanga-zangar dai sun aukawa fadar shugaban kasar dake birnin Bamako ne domin nuna fusatarsu da wani shirin kungiyar ECOWAS da ya tsawaita wa'adin mulkin Mr Traore din daga kwanaki arba'in zuwa shekara guda.

Rahotanni na nuna cewa, an jikkata shugaban rikon kwarya na Malin ne a ka, kuma wata majiyar bangaren kiwon lafiya na cewa, an garzaya da shi asibiti ne a galabaice.

Rahotanni sun ce an sallami Mr Traore din daga asibiti, bayan da gwajin da aka yi masa ya nuna cewa raunukan da ya samu ba munana ba ne.

Likitan da ya duba shi ya ce an tafi da shi cikin wata mota zuwa wani wuri mai cikakken tsaro.

Wadanda suka shaida al'ammarin da idanusnu, sun ce sun ji karar harbin bindigogi, kuma wani kakakin soja ya yi ikirarin cewa masu tsaron lafiya shugaban kasar sun hallaka mutane 3.

Asali

Ana kukan targade amma an samu karaya a Mali, domin wannan harin da aka kai wa shugaban rikon kwarya na kasar ta Mali ya kara girman damuwar da jami'an diplomasiya na yankin ke da ita, wadanda suke ta fadi tashin maido da mulkin demokradiyya a kasar.

Jagororin juyin mulkin sojin da aka yi a watan Maris din da ya gabata sun ce sun yi hakan ne domin gwamnatin lokacin ta kasa dakatar da tawayen da abzinawa ke yi yankin hamadar arewacin kasar.

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Taswirar kasar Mali

Sai dai juyin mulkin da suka yi a babban birnin kasar, ya baiwa Abzinawan karfin gwuiwar kara nausawa.

A yau dai yankin arewacin kasar da ke da fadin da ya fi girman kasar Faransa na hannun Abzinawa da kuma mayaka da ke da kishin Islama.

A karshen makon da ya gabata, kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS ta yi amannar cewa ta samu ci gaba wajen shawo kan shugabannin juyin mulkin kasar na su amince da gwamnatin da za ta jagoranci shirin mika mulki ga farar hula na tsawon shekara guda karkashin jagorancin Diacounda Traore a matsayin shugaban rikon kwarya.

Amma 'yan kasar masu yawa da ba su ji dadin wannan yarjejeniyar da aka kulla a karshen mako ba, sun bazama kan tituna a jiya, sun toshe gadoji tare da kona tayoyi, kuma zanga-zangar tasu ta kai ga wasu daga cikin masu boren sun auka wa ofishin Mr Traore da ke daura da fadar shugaban kasar da aka wawashe a baya, inda suka lakada masa dan karen duka.

Wani mai magana da yawun kungiyar ECOWAS Sunny Ugoh, ya shaida wa BBC cewa, za a iya kara kakaba wa Mali takunkumi idan har ta bayyana cewa sojoji suna da hannu a harin da aka kaiwa shugaban rikon kwarya na kasar.

Kasar Mali ma dai na fuskantar fari da karancin abincin da ya auka wa ilahirin yankin Sahel.

Karin bayani