Za a yanke hukunci a kan kisan Terreblanche

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Eugene Terreblanche

A ranar Talata ce za a yankewa wasu ma'aikatan gidan gona bakaken fata su biyu hukunci bisa zargin da ake yi musu na kashe mai ra'ayin wariyar launin fatar nan na Afirka ta Kudu, Eugene Terreblanche, a shekarar 2010.

Mutanen biyu watau Chris Mahlangu, mai shekaru 29, da wani dan shekaru 18 sun musanta zarge-zargen da ake yi musu wadanda suka hada da na kisan kai da fashi.

An dai tsaurara matakan tsaro a wajen kotun da ake yin shari'ar mutanen biyu wacce ke garin Ventersdorp na arewa maso yammacin kasar.

Kisan da aka yi wa Terreblanche ya kara bijiro da batun wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, shekaru 16 bayan da tsirarun fararen fata suka mika mulki hannun bakaken fata.

Karin bayani