An kama mutane uku kan badakalar James Ibori

 James Ibori
Image caption An yanke wa James Ibori daurin shekaru 13 a Burtaniya

Rundunar 'yan sanda ta birnin London ta tabbtatar da cewar ta kama wasu mutane ukku, dangane da zargin cin hanci da rashawa a shari'ar da aka yiwa tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori.

Daya daga cikin mutanen ukku dan sanda ne, yayin da sauran biyun kuma tsaffin 'yan sanda ne.

Ana zargin dan sandan ne da bayar da bayanan sirri ga wani kamfanin binciken sirri mai zaman kansa da tsohon gwamnan Jihar Delta ya dauka haya domin kare shi a shari'ar da aka yi masa.

Wannan kame dai ya zo ne bayan da aka shaida wa wani kwamitin bincike na majalissar dokokin Burtaniya cewar akwai zargin an baiwa wasu 'yan sanda cin hanci a shari'ar da aka yiwa James Ibori.

Tun a shekarar da ta gabata ne hukumar kula da korafe-korafe akan aikin 'yan sanda ta bukaci Majalissar dokoki ta gudanar da bincike akan zargin cin hanci da rashawa a shari'ar da ake yiwa James Ibori a London.

James Ibori tsohon gwamnan jihar Delta a Najeriya, ya saci daruruwan miliyoyin kudade daga kasarsa.

An kuma yanke masa hukuncin shekaru 13 a gidan yari a Burtaniya, bayan da ya amsa laifin halatta kudaden haram da kuma zamba.

Hukuncin da aka yanke wa Mr Ibori ya ja hankalin masu lura da al'amura a Najeriya, ganin cewa a baya, wata kotun kasar ta wanke shi daga laifuka sama da saba'in da mahukunta a Najeriya suka zarge shi da aikata wa.

Karin bayani