An samu ci gaba a tattauna kan shirin Nukiliyar Iran

Wakilan tattauna batun Nukiliyar Iran Hakkin mallakar hoto a
Image caption Wakilan tattauna batun Nukiliyar Iran

A taron kasashe masu karfin fada-a-ji da ake yi a birnin Baghadaza na Iraqi, an gabatar da sabbin shawarwari a kan yadda za'a kawo karshen jayayya dangane da shirin nulkiyar Iran.

Sai dai kuma har yanzu matsayin Iran yana nesa da na kasashen yamma dangane da batun.

Kakakin kungiyar kasashen Turai, wato EU yace, kasashen dake cikin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da kuma Jamus sun gabatar da wani tayi dake da nufin hana Iran sarrafa makamashi Uranium.

Michael Mann kakakin Cathrine Ashton, mai kula da manufofin hulda da kasashen waje na kungiyar ta EU

Ya ce," mun gabatar da sabon tayi ga Iran domin warware babbar damuwarmu wato sarrafa makamashin Uranium."

Karin bayani