Tunisiya za ta mika tsohon Firayim Ministan Libya ga kasarsa

Al-Baghdadi lokacin da yake kan mukaminsa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Al-Baghdadi lokacin da yake kan mukaminsa

Tunisia ta ce nan ba da jimawa ba za ta mai da firayim ministan Libya na karshe a karkashin mulkin Kanar Gaddafi, Al-Baghdadi Ali al-Mahmoudi, zuwa kasar ta Libya.

Wani babban jami'in gwamnatin Tunisia ya ce za a mai da al-Mahmoudi ne da zarar an kammala shirye-shiryen da suka wajaba.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama dai na adawa da mai da al-Mahmoudi suna masu cewa akwai yiwuwar za a cutar da tsohon dan siyasar na Libya idan aka kai shi gida.

Tun bayan tserewarsa daga Libya bayan kifar da gwamnatin Gaddafi ne dai al-Mahmoudi ya ke kasar ta Tunisia.

Karin bayani