An yankewa wani likita hukuncin daurin shekaru talatin a Pakistan

Osama bin Laden Hakkin mallakar hoto
Image caption Osama bin Laden

Jami'an gwamnatin Pakistan sun ce, wata kotu ta yankewa wani likita hukuncin zaman gidan kaso na shekaru akalla talatin saboda ya tallafawa hukumar leken asiri ta Amurka wato CIA wajen gano mabuyar Osama bin Laden.

Rahotanni na cewa, kotu ta samu da laifin cin amanar kasa.

Shi dai likitan ya gudanar da wani shirin riga kafi na bogi ne wanda kuma ya tallafawa CIA wajen gano maboyar Osama bin Laden a birnin Abbottabad.

Wakilin BBC ya ce a 'yan kwanakin nan jami'an gwamnatin Amurka sun sha yin kiran a saki likitan Shakil Afridi, amma Paskitan ta yanke masa hukuncin zaman gidan kaso mai.

Karin bayani