Yemen na dab da fadawa bala'in yunwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin da a ake yi a Yemen ya yi sanadiyar fuskantar rashin abinci

Wadansu kungiyoyin agaji na duniya sun ce kusan rabin 'yan kasar Yemen na fama da karanin abinci saboda halin rashin zaman lafiyar da kasar ke ciki.

A wata sanarwar gargadi ta hadin gwiwa da kungiyoyin agajin guda bakwai suka fitar, sun ce mutane miliyan goma, watau kashi arba'in da hudu cikin dari na 'yan kasar, na fama da rashin abinci mai gina jiki.

A cewarsu, mutane miliyan biyar daga cikinsu na bukatar kulawar gaggawa.

Kasar Yemen dai ta yi fama da zanga-zangar masu son tabbatar da mulkin dimokaradiyya; da kuma rikici tsakanin kabilu a arewaci, da ma fadace-fadace tsakanin 'yan kungiyoyin Musulunci da ke kudancin kasar.

Taron kasashen duniya a kan Yemen

Wannan gargadi da kungiyoyin agajin suka yi dai ya zo ne kwana guda gabanin taron da kasashen duniya za su gudanar game da Yemen.

Kasashen duniya, wadanda suka yi wa kansu lakabi da 'abokan Yemen' da ke taro a baban birnin Saudi Arabia ranar Laraba, suna mayar da hakali ne a kan yanayin tabarbarewar tsaron da kasar ke ciki da kuma yadda za a samu sauyin siyasa.

Sai dai kungiyoyin agajin wadanda suka hada da CARE, International Medical Corps, Islamic Relief, Merlin, Mercy Corps, Oxfam da kuma Save the Children, sun ce mayar da hankali da kasashen suka yi a kan rikici da siyasa ya sanya an ki daukar matakai na magance talauci da yunwar da 'yan kasar ke fama da su.

Karin bayani