Jam'iyyar 'yanuwa musulmi tace tana kan gaba a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters

An kammala zagayen farko na zaben shugaban kasa a Masar kuma an kidaya kusan dukka kuri'un da aka kada.

Jam'iyyar 'yan uwa musulmi tace dan takarar ta Mohammed Morsi ne ke kan gaba zuwa yanzu.

Tsohon Fryministan kasar Ahmad Shafik shine na biyu, yayinda kuma aka ruwaito cewa Hamdeen Sabbahi, dan jamiyyar gurguzu shine ke na ukku.

Idan babu dan takarar da yayi rinjaye to zaa je zagaye na biyu tsakanin na daya dana biyu.

A farkon mako mai zuwa ne ake saran samun samakon zaben.

Kimanin kashi hamsin cikin dari ne na wadanda aka yiwa rajista suka yi zaben