Shan inna annoba ce a duniya in ji WHO

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cutar shan inna a matsayin annobar kiwon lafiya a duniya.

Hukumar ta ce an samu karuwar barkewar cutar a kasashen Turai da Afirka da Asia a cikin shekaru biyun da suka gabata.

A cewar hukumar yunkurin da ake yi na kawar da cutar, yanzu ya kai matsayin da zaa ce kodai zaa yi nasara ne ko kuma a kasa kwata-kwata.

Sai dai kuma ta ce yadda India ta yi nasara wajen kawar da cutar ta Polio, ta hanyar samun isassun kudade na tafiyar da allurar rigakafi, wata alama ce dake nuna cewa a sauran kasashe ma zaa iya yin hakan.

Har yanzu dai cutar ta Polio ta kasance annoba a kasashen Afghnaistan da Pakistan da kuma Najeriya.