An cimma yarjejeniya akan lokacin zabe a Somalia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Shugabannin hauloli daban-daban na Somalia sun amince da wani jaddawali da zaa yi aiki da shi wajen zabar sabon shugaban kasa nan da ranar 20 ga watan Agusta mai zuwa.

Wannan 'yarjejeniya mai cike da tarihi dai, ta zo ne bayan da aka shafe kwanaki uku ana zazzafar tattaunawa a Ethiopia.

Shidda daga cikin shugabannin haulilin ne suka halartci taron.

Sai dai kuma kungiyar masu tsattsauran kishin Islama ta al Shabab, wadda ke iko da galibin sassan kasar ta Somalia, ba ta sa hannu a 'yarjejeniyar ba.

Kasashe da kungiyoyi masu bada agaji sun yi barazanar janye kudaden da suke bayarwa, muddin baa cimma 'yarjejeniya ba kan yadda zaa kawo karshen rikicin siyasar da aka shafe kusan shekaru 20 ana yi a kasar.