An kaddamar da madubin hangen nesa mafi girma a duniya

Kasashen Australia da Africa ta kudu sun samu nasarar karbar bakuncin inda zaa kafa madubin hangen nesa da ya fi kowanne girma a duniya.

Aikin zai kunshi kafa na'urorin dauka da watsa bayanai dubu ukku wadanda za'a hada su da wata katafariyar na'ura mai kwakwalwa wadda zata dunga dauko bayanai daga gungun taurarin da ke zagaya duniya.

Masana ilimin kimiyya na fatan cewar wannan madubin hangen nesa zai amsa wasu daga cikin manya manyan tabbayoyin da ake yi akan duniya da sararin samaniya da ma kuma yiwuwar samun halittu masu rai a wasu duniyoyin.