Dakarun AU sun kwace garin Afgoye na Somalia

somalia Hakkin mallakar hoto s
Image caption Dakarun AU a Somalia

Dakarun kungiyar Tarayyar Afrika-AU sun ce sun karbe iko da garin Afgoye mai muhimmanci daga kungiyar Al-Shabbab.

Wani kakkakin dakarun ya shaidawa BBC cewa mutanen garin sun fito kan tituna don yiwa dakarun nasu kyakyawayar tarba.

Garin na Afgoye dai yana da nisan kilomita 30 ne daga arewa maso yammacin Mogadishu, babban birnin Somalia, kuma wata muhimiyar mahada ce ta wasu manyan hanyoyi biyu.

Ta farko tana zuwa garin Baidoa ne na arewa maso yammacin kasar, hanya ta biyun kuma tana kaiwa ga garin Kismayo mai tashar jiragen ruwa, wanda har yanzu wata matattara ce ta masu fafituka na kungiyar Al Shabaab.

Kama garin na Afgoye dai, wani babban komabaya ne ga kungiyar ta al Shabaab saboda yanzu garin ya raba yankunan dake karkashin ikonsu zuwa na Arewa da na Kudu.

Laftana Kanar Paddy Ankunda, shi ne kakakin rundinar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afruka a kasar ta Somalia "a ganina Afgoye ita ce matattara ta biyu mafi girma ta masu fafutika na kungiyar al Shabbab, bayan Kismayo, mahada ce mai muhimmancin gaske".

Yanzu dai masu sharhi na ganin cewa muhimmjin fada na gaba da zaa yi, shi ne na kwato garin Marka, wanda ke da nisan kilomita 90 daga kudancin garin na Afgoye.

A farkon wannan shekarar ne dai, Majalisar Dinkin Duniya ta amince ta kara yawan dakarun kiyaye zaman lafiya, na Tarayyar Afrika a Somaliar daga dubu 12 zuwa kusan dubu 18 don su hada da sojojin Kenya, wadanda suka kutsa cikin Somalia a cikin watan Oktoba domin farautar 'yan kungiyar Al-Shabaab.

Karin bayani