Ta yaya rikicin tattalin arzikin Turai zai shafi Afrika

Eurozone Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tattalin arzikin kasashen Turai na cikin mawuyacin hali

A halin hanzu kashi daya bisa uku na kayayyakin da Afrika ke fitarwa tana kaisu ne zuwa kasashen Turai. Haka kuma Afrika na samun fasaha da ayyukan kwararrun da take takama da su daga nahiyar Turai, sai dai wadannan abubuwa na iya fuskantar koma-baya sakamakon rikicin tattalin arzikin Turan.

Don haka koma-baya a tattalin arzikin Turai zai haifar da raguwar kayayyakin da Afrika ke fitarwa.

Kuma duk wani koma-baya a kudaden da ake samu daga kasashen waje, musaman a yankin kudu da sahara, to babu shakka zai haifar da mummunar illa ga jama'ar yankin.

Babu makawa, illar za ta banbanta daga kasa-zuwa-kasa - adadin kayan da kasa ke fitarwa zuwa Turai da kuma ingancin manufofin tattalin arzikinta.

Akwai illoli da dama

Baya ga raguwa wurin adadin kayan da ake fitarwa, akwai wasu ababen damuwa ganin yadda Turai ke fadi-tashin shawo kan matsalar basukanta:

. Yiwuwar rage tallafi daga kasashen waje saboda kasashen Turai na kokarin tallafawa matasansu da basu da aikin yi da kuma sauran bukatu na yau da kullum.

. Raguwa wurin kudaden da ake aikowa da su Afrika saboda 'yan nahiyar da ke zaune a Turai, za su fuskanci rashin aikin yi a Turai.

. Raguwar kudaden shiga ta fannin yawon bude ido, saboda Turawa na fama da matakan tsuke bakin aljihu.

. Koma-bayan tattalin arziki baki daya: Hukumar kula da ci gaban tattalin arziki ta OECD, ta yi hasashen cewa kayayyakin da nahiyar Afrika ke samarwa za su fuskanci koma-baya da kashi 0.7 da kuma 1.2 a 2012 da kuma 2013.

Dukka wannan koma-baya ne ga nahiyar da ke dauke da kashi daya bisa uku na talakawan duniya, da rashin katabus wurin cimma muradun karni (MDGs).

Wasu kasashen za su iya kai labari

Sai dai duk da haka, kasashen Afrika da ke da ci gaba da kuma kyakkyawan tsari, ka iya jawo hankalin masu zuba jari sakamakon matsalar da ake fuskanta a Turai.

Alal misali, Afrika ta Kudu da Ghana da ke da zaman lafiya, ka iya samun masu zuba jari fiye da Masar da Mali wadanda ke fama da rikice-rikice.

Baya ga haka, fannin ma'adanai na Afrika zai ci gaba da jan hankalin masu zuba jari daga Turai da kuma wasu wuraren saboda alfanun da ake samu daga fannin.

Hakan ne kuma ya sa Najeriya, ke ci gaba da samun masu zuba jari a fannin mai da iskar gas, duk kuwa da tashin hankalin da ake fama da shi a kasar.

Matsalar ita ce zuba jari a fannoni masu kawo riba sosai bai fiye yin tasiri kan rayuwar talakawa ba.

A takaice, ya kamata Afrika ta tashi tsaye wurin tunkarar koma-bayan tattalin arzikin da ake fuskanta a duniya ta hanyar shimfida manufofin da za su bunkasa sauran fannonin tattalin arziki, da ayyukan ci gaba, da inganta ayyukan gwamnati da bunkasa alaka tsakanin yankunan nahiyar.

Karin bayani