Mutane 20 ne su ka mutu a rikicin Mali da Burkina Faso

Akalla mutane ashirin da biyar ne suka mutu a wani rikici daya barke a kan iyakar Burkina Faso da kasar Mali.

An dai shafe kwanaki kenan ana tashe tashen hankula a kan iyakar kasar Mali sakamakon wata takaddama da ake yi kan gonaki da kuma wuraren kiwo tsakanin kabilar Fula da 'yan kabilar Dogon.

Rahotanni sun ce yarjejeniyar da bangarorin biyu su ka cimma a baya ta ruguje tun bayan juyin mulkin daka yi a kasar Malin watanni biyu da suka gabata .