Rashin jituwa tsakanin Amurka da Pakistan

zardari Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Pakistan, Asif Zardari da Hillary Clinton

Rashin jituwar dake tsakanin Amurka da Pakistan na kara kazancewa bayan Pakistan din ta daure wani likitan da ta zarga da taimakawa Amurka da bayanan sirri akan Osama bin Laden.

Lamarin dai yanzu ya sa duk wata maganar sasantawa tsakanin kasashen biyu zata yi wuya, ganin yadda bakin jinin Pakistan ke karuwa a tsakanin 'yan majalisarar dokokin Amurka.

Batun kashe Osama Bin Laden da dakarun Amurka su ka yi a Pakistan na cigaba da shafar dangantaka tsakanin Washington da Islamabad.

Kusan ma abubuwa na kaara tabarbarewa ne a lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke da muhimmanci sosai a garesu.

Yawan matsalolin na cigaba da karuwa ne, saboda baya da batun kashe Bin Laden, akwai batun kai hare-haren da jirage marassa matuka da Amurkan ke kaiwa a yankunan Pakistan din.

Ga kuma kashe dakarun Pakistan din da Amurkar ta yi akan kuskure a wani harin jirgin saman da takai, wanda har yanzu basu nemi afuwa daga Pakistan dimba.

Maida martanin da Islamabad ta yi na hana bi ta Pakistan wajen kai kayan yakin NATO a Afghanistan da kuma daure, Dr Shakil Afridi, mutumin da ya taimaki Amurkawan suka kashe Bin Laden sun hayaka Washington sosai.

Kwamitin majalisar dattawan Amurkan ya yanke yawan kudin taimakon da Amurkan ke baiwa Pakistan.

'Rage yawan tallafi'

Amurka ta zabce dala miliyan 33 a kowace shekara da take baiwa Pakistan tallafi, don nuna fushinta akan daure Dr Afridin da akayi.

Sakatariyar harkokin wajen Amurkar, Hillary Clinton, ma ta bayyana damuwa akan daure Dr Afridin. Amma ta yi nuni da cewa Amurkan na yi shawarwari da Pakistan din akan batutuwa da dama.

Misii Clinton tace: "Muna tsakiyar tattaunawa da gwamnatin Pakistan akan batutuwa dabam dabam, wadanda ke muhimmaci sosai ga Amurka da sauran kasashen duniya".

Neman samun jituwa tsakanin kasashen biyu na iya cin tura, idan shugabannisu basu dage wajen samun nasarar hakan ba.

Amurkan ta gayyaci Shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari a taron NATO da aka yi kwanan nan a Chicago -- wani matakin da ake ganin cewa zai taimaka wajen rage rashin jituwa.

To amma da ba a samu wata kyakyawar yarjejeniya ba, sai Shugaba Obama yayi burus dashi.

Karin bayani