An nuna shakku kan sahihancin zaben Masar

Zaben kasar Masar
Image caption Zaben kasar Masar

Daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a Masar da ba basuyi nasara ba a zagayen farko, Hamdeen Sabahi yayi kira da asake kirga wasu kuri'un da aka kada saboda acewar sa anyi magudi.

Wani kakakin sa ya ce zai shigar da kara ranar Lahadi don hana gudanar da zagaye na biyu na zaben.

A daya bangaren kuma, wanda ake cewa shi ne ya zo na biyu a zaben, kuma tsohon Praministan Masar, Ahmed Shafiq yace zamanin shugaba Mubarak ya wuce har abada.

"Yace abunda ya wuce ya wuce.

Bazamu yi fada da juna ba, zamu yi aiki ne tare kuma ina amfanin komawa zamanin da ya wuce.

An samu sauyi a Masar kuma babu wanda zai maida hannun agogo baya".

Tsohon shugaban Amurka, Jimmy Carter da ke jagorantar wata tawagar masu sa ido yace koda yake ba' a barsu sun je ko ina ba, amma ya gamsu da tsarin da aka yi

Karin bayani