Kokarin inganta layukan salula a Najeriya

Taswirar Njeriya
Image caption Taswirar Njeriya

A Najeriya, wasu rahotanni sun ce har yanzu babu tabbaci game da kawo karshen takaddama tsakanin manyan kamfanonin dake samar da layukan wayar salula da Hukumar lura da harkokin sadarwar kasar NCC,kan wa'adin da ta ba su , na su biya masu amfani da layukansu diyyar kudi sama da Naira miliyan dubu daya, sakamakon abinda hukumar ta ce rashin ingancin layukan nasu.

Rahotanni dai sun ce a jiya ne kamfanonin layukan wayar suka yi wata ganawa,wacce kuma ta zo daidai da cikar wa'adin da hukumar ta NCC ta debar musu su biya diyyar.

Dama dai jama'a da dama sun dade suna kokawa da matsalolin da sukan fuskanta a layukan wayayin su.

Karin bayani