Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da kisan Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Sakatare Janar din Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon da kuma Mazon kasashen duniya a Syria Kofi Annan, sun yi tur da kisan sama da mutane sittin da aka yi a Syria.

A cikin gawawwakin da aka gano har da na kananan yara sama da talatin a garin Houla.

Maso sa'ido na Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da cewa hare-haren takunan yaki ne da kuma makaman artillery da aka yi a wata unguwa da mutane ke zama ya janyo dumbin asarar rayukan da aka samu.

A cikin wata sanarwa da su ka fitar sun su soki kisan gillar da su ka ce an yi a Syria inda su ka bayyana lamarin a matsayin abun tashin hankali da kuma kazamin laifi ta hanyar amfani da karfi.

Sanarwar ta kara da cewa wannan al'amari ya sabawa dokar kasa da kasa.

Sanarwar da Mista Ban da Mistan Anan su ka fitar sun bukaci gwamnatin Syria da ta gaggauta daina amfani da manyan makamai a yankin.

Har wa yau sun yi kira da aka tsaiga wuta a duk fadin kasar.

Fadar gwamnatin Amurka ma ta yi tur da lamarin, inda ta ce mumunar hari ne a kan kaddamar a kan biladama.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Amurka ya ce wanan harin na nuni da cewa gwamnatin Syria ba hallaltaciya ce ba, saboda gwamnatin kasar na amfani da karfin tuwo wajen murkushe zanga zangar lumana.