Matsalar Turai na iya janyowa Afrika cikas

euro Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kudin Tarrayar Turai- Euro

Ci-gaban tattalin arzikin Afrika ya dan sami cikas daga juyin juya-halin da aka samu a kasashen Laraba shekarar da ta gabata, in ji Bankin Ci-gaban Afrika.

Bisa haka, ci-gaban Afrikar ya yi baya daga kashi 5 cikin dari a shekara ta 2010 zuwa kashi 3.4 cikin dari a 2011.

Kana bankin ya yi gargadin cewa, Afrikar za ta sami mummunan cikas a bana, idan har matsalar tattalin arzikin kasashen Turai ta kara kamari.

Idan dai sauyin da aka samu a kasashen labarawa ne ya raunata habakar tattalin arzikin nahiyar Afrika a bara, to a bana matsalar Turai ce za ta shafi Afrikan.

Wahalolin da Turai ke fuskanta za su kawo raguwar kudaden da Afrikan ke samu wajen sayar da kayayyakinta da kuma na wajen harkar bude ido.

Za su kuma rage yawan agajin da suke samu daga kasashen duniya, da kuma yawan kudin da 'yan Afrika mazauna Turai ke aikawa gida.

Rahoton wannan shekarar ya maida hakali ne akan matasan Afrika. Nahiyar tafi ko-ina yawan matasa a duniya, inda take da kimanin matasa milyan 200, yan shekaru 15 zuwa 24.

Yawansu kuma na karuwa da sauri, har zai linka biyu nan da shekara ta 2045.

Bankin ya yi gargadin cewa, idan kasashen Afrikan basu sabunta fasalin tattalin arzikinsu ba, to za su yi asarar amfana daga matasan.

To amma akwai wasu abubuwan ban sha'awa ma da ba'a fito dasu fili ba a wannan dogon rahoto.

Bankin ya yi nuni da cewa a harkar kere-kere, ko kasashen da sukafi cigaba a Afrikan ma, ba za su iya yin gasa da China da India ba.

Babu wuyar ganin dalilin hakan: kudin albashi a kasashen Afrika ta Kudu da Mauritius sun zarce na China da India fintinkau, wadanda ke biyan sulusi koma rubi'in binda na Afrikan ke biya.

'Hasashe akan wasu kasashe'

A kimantawar da yayiwa kasa-da-kasa, Bankin yace tattalin arzikin Nijer ya raunana sosai saboda matsalar farin da aka samu, da kuma rikice-rikice a kasashen Ivory Coast da Nigeria da kuma Libya masu makwanbtaka da ita.

To amma tattalin arzikinNijer din zai iya habaka cikin hanzari a bana saboda cigaba da kasar ta samu a harkar man fetur.

Cigaba da ta samu na kafa matatar mai a Zinder a karshen shekara ta 2011 zai tallafama harkar fitar da mai, ya baiwa Nijer din damar zama cikakkar kasar dake saida mai a bana.

An kiyasta cewa a banar tattalin arzikin kasar zai bunkasa da fiye da kashi 11 bisa dari.

Bankin kuma yace tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa a bara, domin karuwar harkokin da basu shafi man fetur ba, musamman ma harkokin sadarwa, da gine-gine, da cinikayya da harkokin otel-otel da kere-kere da kuma aikin gona.

Yace hasashe ya nuna cewa a 'yan shekaru masu zuwa ma, abubuwa za su yi kyau, koda yake dai za a cigaba da fama da matsalar rashin aikin yi, inda kusan rubu'in 'yan Najeriyar basu da aikin yi. Bankin ya kiyasta cewa tattalin arzikin kasar zai bunkasa da kusan kashi bakwai bisa dari a bana.