Sa ido kan kasafin kudin babban bankin Najeriya

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Taswirar Najeriya

Wani kwamitin majalisar dattawan Najeriya ya soma sauraron ra'ayoyin jama'a game da kwaskiramar da wani dan majalisar dattawan kasar ya nemi a yi.

Yana so ne a yi wa dokar da ta kafa babban bankin kasar gyara ne kan ikon da a da yake da shi, yadda yanzu sai ya nemi amincewar majalisar dokokin kasar wajen shiryawa da kuma aiwatar da kasafin kudinsa.

A baya dai Babban bankin Najeriya yana da 'yancin tsara kasafin kudin sa ne ba tare da neman amincewar 'yan majalisar ba, abin da wasu a majalisar ke son ganin an sauya.

Karin bayani