Annan ya kadu akan kashe mutane a Syria

annan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kofi Annan gaban maneman labarai

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kan kasar Syria, Kofi Annan, ya isa birnin Damaskas, inda ya ce, ya yi matukar kaduwa a kan kisan mutane fiye da dari, kusan rabi kananan yara, a garin Haula.

Zai kuma yi tattaunawar keke-da-keke gobe Talata da shugaban Syriar, Basharul Assad.

A bayyane dai ministan harkokin wajen Rasha da sakataren harkokin wajen Burtaniya sun nuna kamar sun cimma yarjejniya a yau da safe, cewa yin aiki da tsarin zaman lafiyan na Kofin Annan shine kawai abinda zai warware rikicin Syrian.

To amma a tattaunawar da suka yi a asirce, akwai rashin jituwa.

William Hague ya dora laifin kashe-kashen da akayi a Houla akan gwamnatin Syria.Ya yi gargadin cewa idan shirin samar da zaman lafiyar bai yi aiki ba, za a fuskanci yakin basasa.

To amma Sergei Lavrov cewa yayi ba gwmantin Syriar kadai za a dorawa laifi ba. Ya ce kungiyoyin 'yan adawa ma masu amfani da makamai suna da laifi.

Ya kuma musunta zargin cewa Rashan ta dukufa ne kawai tabbatar da kasancewar Shugaba Assad akan mulki.

Lavrov yace: "Mu a wajen mu ba wanda ke kan mulki a Syria bane abu mafi muhimmanci. Mu abinda muke so shine a samar da hanyar kawo karshe tashin hankali, domin a daina kashe jama'a".

Shi kanshi Kofi Annan da ya isa Damascus a yau din ya bayyana damuwa sosai akan irin kashe-kashen da aka yin. Ya ce kuma dole a hukunta wadanda suka aikata su:

Annan yace: "Kwamitin tsaro ya roki Majalisar Dinkin Duniya ta da cigaba da binciken hare-haren da aka kai a Houlan. Dole ne a hukunta wadanda suka tabka wadannan munana laifuka. Na faminci cewa gwamnati ta fara bincike".

Gwamnatin Syrian dai da musunta cewa tana da hannu a kashe-kashen. Amma 'yan adawa sun yi zargin cewa har yanzu ma gwamnati na kai hare-hare a wasu wuraren.

Karin bayani