Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da harin Houla

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fadan Syria

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tir da amfani da manyan makaman yaki da gwamnatin Syria ta yi a garin Houla.

A harin an aka kashe fiye da mutane dari ciki har da kananan Yara a ranar jumma'a.

Wata sanarwa da kwamitin sulhun ya bayar ta ce an harba manyan harsasai da tankokin yaki da bindigogin artilery a kan garin, abinda ta ce amfani ne da karfin da ya zarce kima a kan farar hula abunda acewar kwamitin ya sabawa dokar kasashen duniya.

Sai dai Jakadan Syria a Majalisar Dinkin duniya, ya musanta cewa gwamnatin Syria ce ta kai harin a birnin Houla.

Karin bayani