Girgizar kasa ta kashe mutane 10 a Italiya

italiya Hakkin mallakar hoto d
Image caption Girgizar kasa a Italiya

Akalla mutane goma ne suka mutu a girgizar kasa data sake abkuwa a arewacin kasar Italiya, fiye da mako guda bayan da wasu mutane bakwai suka mutu a girgizar kasar data fara abkuwa a yankin.

Rahotanni sun ce yanzu haka ma, akwai wasu mutane da suka makale a burbushin gine-gine.

Hukumar binciken yanayin karkashin kasa ta Amurka ta ce karfin girgizar kasar ta kai maki biyar da digo takwas, kuma cibiyarta, nada nesan kilomita 45 daga arewa maso yammacin Bologna.

Prime Ministan Italiyan Mario Monti ya nuna takaicinsa game lamarin.

Monti " Ina son in tabbatarwa kowa da kowa, cewa gwamnatin Italiya zata yi dukkan mai yiwuwa cikin kan kanin lokaci don ganin ta samar da yanayin ci gaba, da rayuwa kamar yadda ya kamata a wannan yankin".

Karin bayani